Babbar jam’iyyar hamayya ta CPC a Nigeria ta shigar da kara a kotun sauraren kararrakin zaben Nigeria. A ran lahadi wadda ita ce ranar karshen ta karbar kararrakin zaben Nigeria, da misalin karfe 4:30 na la’asar agogon Nigeria, shugaban jam’iyyar CPC na kasa, Prince Tony Momoh, ya jagoranci sauran jami’an jam’iyyar CPC da lauyoyin jam’iyyar zuwa harabar kotun daukaka kara ta tarayya kafin a rufe karbar kararrakin zaben.
Dan takarar kujerar shugaban kasa a zaben shugaban Nigeria da aka gudanar ran 16 ga watan Afrilun da ya gabata, Janar mai ritaya Muhamadu Buhari shi ya shiagar da karar ta kan jam’iyyarsa ta CPC wadda yayi takarar a karashin inuwarta.Anji shugaban jam’iyyar ta CPC Tony Momoh yana cewa jam’iyyar tana bukatar a sake gudanar da zaben shugaban Nigeria a jihohin Nigeria 20 dake cikin shiyyoyi shida na Nigeria.
Haka na faruwa ne a dai dai lokacin da mataimakin shugaban Nigeria karkashin inuwar jam’iyyar PDP Namadi Sambo shima ya kammala nasa shirin na kalubalantaar karar da jam’iyyar CPC ta shigar a hukumar jin kararrarakin zaben Nigeria. A tattaunawar da babban sakataren jam’iyyar CPC Buba Galadima yayi da wakilin sashen hausa na Muryar Amurka, Nasiru Adamu el-Hikaya a birnin tarrayar Nigeria, Abuja, anji yana cewa jam’iyyar CPC ce ta shigar da karar ba dan takarar jam’iyyar janar Buhari mai ritaya ba.
Jami’an kallon kasa da kasa, da na cikin gida, sun amince da cewa zaben shugaban Nigeria na ran 16 ga watan Afrilu nada sahihanci kuma shine irinsa na farko da aka gudanar cikin ‘yanci da walwala. Shugaba Goodluck Jonathan, daga yankin kudancin Nigeria, ya sami nasarar zaben inda ya kada dan takara Muhammadu Buhari wanda ya fito daga Arewacin Nigeria. Sai dai anyi tarzoma bayan bayyana sakamakon zaben shugaban kasar Nigeria, rahotanni suka ce akalla mutane dari biyar ne suka halaka.