Hukumar bunkasa ilimin fasahar sadarwa ta Najeriya NITDA, ta rattaba hannu akan wata yarjejeniyar aiki tare da cibiyar Mass Challenge mai kula da harkokin fasahar sadarwa dake Amurka, domin bunkasa tattalin arzikin Najeriya ta wannan fannin.
Cibiyar Mass Challenge dake jihar Boston a Amurka na ayyukan bincike da jagoranci da kuma tallafawa matasa masu basirar kirkire-kirkire a fannin ilimin fasahar sadarwa ta zamani a kasashen duniya daban-daban da nufin bunkasa tattalin arziki ta yin amfani da ilimin fasahar sadarwa.
Hajiya Hadiza Umar kakaki a hukumar ta NITDA ta yi karin bayani game da yarjejeniyar da cibiyar Mass challenge ta na mai cewa fatansu shi ne Najeriya ta zama kan gaba a fannin fasahar sadarwa a nahiyar Afirka gaba daya.
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke cewa ya kamata hukumar ta NITDA ta warware wasu kalubale da suka shafi ayyukanta.
Ga alama dai hankulan ‘yan Najeriya na kara karkata akan aikace-aikacen wannan hukuma ta NITDA la’akkari da ci ga da tasirin da ilimin fasahar sadarwa ke yi ga rayuwarsu ta yau da kullum.
Saurari rahoto cikin sauti daga Mahmud Ibrahim Kwari:
Your browser doesn’t support HTML5