Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Najeriya Zata Kafa Sansanoni Domin Ambaliyar Ruwa

Mutane suke kokarin tserewa daga ambaliyar ruwa a a wasu sassan Najeriya.

Duk da cewa daminar bana tazo karshe hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya zata bude sansanoni a yankunan da ake fargabar cewa zasu fuskanci ambaliya a jihar Adamawa.
Duk da cewa damina ta fara janye jiki bana, hukumomi a jihar Adamawa suna ci gaba da gargadi ga mutane da suke zaune a wurare da ake faragabar zasu fuskanci ambaliar ruwa a bana.

Hukumar bada agajin gaggawa ta bakin babban jami'inta a shiyyar arewa maso gabashin kasar ya gayawa wakilin Sashen Hausa cewa hukumar ta himmatu wajen ganin ta dauki matakin riga kafi domin kaucewa irin matslar da aka fuskanta a bara.

A gefe daya kuma gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamna Murtala Nyako tana kara gargadi ga mutane su kwana cikin shiri, kuma su kaucewa matakai d a zasu assasa matsalar ambaliya.

Your browser doesn’t support HTML5

NEMA zata dauki matakai domin kare jama'a daga ambaliyar ruwa.