Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Asarar Da Ambaliyar Ruwa Ya Haddasa Bara A Najeriya


Hotun ambaliyar ruwa a Jihar Bauci
Hotun ambaliyar ruwa a Jihar Bauci

Hukumar bada agajin gaggawa ta tantance yawan asarar rayuka da dukiyoyi da kasar ta yi bara sanadiyar ambaliyar ruwa

A Najeriya hukumar dake bada agajin gaggawa ta bada addadin asarar rayuka da dukiyoyi da kasar ta yi sabili da ambaliyar ruwan bara.

Sanarwar da hukumar bada agaji cikin gaggawa ta bayar shugaban hukumar Alhaji Mohammed Sani Sidi ya ce bara kasar ta rasa rayuka 360 kana ta yi asarar dukiyoyi na Nera 2.6 trn. Ya bada sanarwar ne a taron manema labarai da ya yi yayin da ya ziyarci Bauchi. Ya zo Bauchi ne ya gani da idonsa barnar da ambaliyan ruwa ya yi da kuma raba kayan agaji ma wadanda abun ya shafa a wannan shekarar.

Ya ce sun kafa sansanoni daban daban a wurare da dama domin kawo doki da kuma guje ma yin anfani da makarantu da masallatai da coci- coci.Ya bada misali da wanda suka kafa a Kirfi inda harma makaranta da asibiti da rijiyar burtsatsi suka gina a wurin. Ya ce kullum suna kara kwarewa ne. Sun yi koyi da ambaliyar ruwan da aka yi bara wanda ya ce shi ne irinsa na farko a kasar. Amma a wannan shekara sun kware sosai sun kuma yi duk irin shirin da ya kamata su yi. Duk wuraren da suka gina za'a kai kayan abinci da kayan shimfida da magunguna.

Mukaddashin gwamnan Bauchi Alhaji Sagir Aminu Saleh ya bayyana shirin gwamnatin Bauchi dangane da ambaliyar ruwa dake addabar jihar. Gwamnatin jihar ta tura jami'anta duk kananan hukumomi su kaiyade irin matsalar da aka samu a wurare daban daban. A wasu wuraren ambaliyar ruwa ya narke gidaje domin irin gine-ginesu.Wasu gonakai ruwa ya mamayesu. Duk irin wadannan suka turawa hukumar agajin gaggawa ta kasa. A jihar hukumar ta jiha ta bada agajin gaggawa kuma ana cigaba da yi.

Sai dai mutane na korafin cewa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa bara sai bana a ka biya su diyar da bata taka kara ta karya ba. Misali wanda ya yi asarar gonakai da gidaje an bashi nera dubu daya da dari biyar bayan shekara daya.

Ga karin rahoto.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG