Kawo yanzu akalla kauyuka shida ambaliyar ruwa ya cinye a jihar Bauchi. An yi asarar gidaje da dukiyoyi amma babu rayuka da suka salwanta. Jami'in hukumar bada agajin gaggawa ya ce kawo yanzu gidaje fiye da dubu daya da dari biyu suka zama babu su kuma an yi asarar dukiyoyin da suka fi nera miliyan talatin.
Hukumar ta yi anfani da makarantu ta tsugunar da wadanda suka rasa muhallansu. Ita kuma hukumar agaji ta kasa ta dauki kidigdiga tana kokarin kawo doki.
Da alama dai jami'an jihar Bauchin sun yi sakaci da gargadin da masu harsashen yanayi suka bayar inda suka fada karara cewa za'a samu ambaliyar ruwa a wannan shekarar fiye da bara. Babu wani shiri da jihar ta yi domin dakile ko rage aukuwar ambaliyar ruwa.
Ga karin bayani.