WASHINGTON, DC —
Dama masanan yanayi sun jama kasar Najeriya kunne cewa za'a yi mugun ambaliyar ruwa a kasar fiye da abun da ya faru bara.
Sai gashi hukumar dake bada agajin gaggawa a Najeriya reshen dake kula da jihohin Bauchi, Gombe, Taraba da Adamawa ta ce an samu ambaliyar ruwa a karamar hukumar Bajoga wanda ya yi sanadiyar rushe gidaje fiye da dari biyar makon da ya gabata. Jami'in hukumar Mr Apollo Dediye shi ya bayyana hakan. Ya ce lamarin ya faru ne ranar Lahadi yayin da aka kwana ana ruwa kamar da bakin kwarya. Wajen mutane 517 lamarin ya shafa amma babu rai da ya salwanta sai dai mutane sun ji ciwo musamman wadanda ke cikin wasu gidaje 160.
Dangane da kawowa mutane doki jami'in ya ce zasu aika da rahotonsu zuwa hedkwarsu domin a kawo taimako. Karamar hukuma da gwamnatin jihar na iyakacin kokarinsu. Wadanda suka rasa muhallansu kuma an tanada masu wuri. Tsananin ruwan sama shi ne sanadiyar ambaliyar ba wai mutane sun yi wani abun da bai kamata ba.
Ga karin bayani daga Abdulwahab Mohammed.