Hotunan Yara Kankana a Iraqi Dake Cikin Mawuyacin Hali Da UNICEF Ta Fitar
Wani dan gudun hijira mai suna Ibrahim Makhool na dauke da hotunan gidansa da hare-haren jarigen sama suka rusa a lokacin da ake kaiwa 'yan ta'addan IS hari a watan Disamba, harin da ya kashe biyu daga cikin yaransa uku a garin Hammam Alill dake Iraqi, ranar Laraba 21 ga watan Yuni shekarar 2017.
Bayan da ya rasa 'ya'yansa a yakin na IS, wannan 'yar mai suna Zamin ita kadai ta rage ma Ibrahim Makhool, wacce ta yi magana akan yadda take son tsohon gidansu yayin da suke gudun hijira, inda ta ce gidan ya na da ban sha'awa kuma "ina so in tafi gida."
Umm Saja tare da iyalanta sun iso a wani asibiti dake babban birnin Mosul a Iraqi ranar 21 ga watan Yuni, bayan gujewa hare-haren sama na kungiyar IS. 'Yarta Saja mai shekara daya na fama da matsalar yunwa lamarin da ya sa ta rame har likitoci suka kasa samun jijiya a jikinta.
Ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kulla da yara kanana UNICEF ya ce yara fiya da dubu daya ne suka mutu sanadiyar rikicin IS a Iraqi inda inda aka kwashe shekaru uku ana fada aka kuma raunata mutum sama da dubu 1,300. Wadan adadi ne kadai da su suka sani a Mosul, Iraqi, Yuni 21, 2017.
Likitocin sun ce yara kanana da kuma masu yawan shekaru sun fi fuskantar matsalar rashin abinci da tsabtataccen ruwan sha saboda yakin Iraqi, sannan sun fi fadawa hadarin a jikkata su yayin da iyalai ke tserewa harbe-harben mayakan IS.
Wannan wani lokaci ne da likitoci ke kokarin yi wa Saja mai shekara guda allura sa'oi kadan bayan da iyalanta suka tsere daga yankunan IS a Mosul dake Iraqi a ranar 21 ga watan Yunin shekarar 2017. Sun kuma ce har a yankunan da hukumomin Iraqi ke rike da su, yara na fama da annobar amai da gudawa saboda rashin tsabtataccen ruwan sha.