Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dole Ne Sojojin Najeriya Su Sake Salon Yaki Da Boko Haram- Isa Kontagora


Kanal Aminu Isa Kontagora yace akwai bukatar mutane su tashi tsaye, su cigaba da taimakawa jami'an tsaro da bayanan sirri don a samu a yi nasara da 'yan Boko Haram.

A cikin ‘yan kwanakin nan ‘yan hare-haren kungiyar boko haram a arewa maso gabashin Najeriya na karuwa abinda ke jefa alamar tambaya akan kokarin da dakarun Najeriya ke yi wajen murkushe mayakan.

Masanin dabarun yaki kuma tsohon gwamnan mulkin soja a jihohin Kano, da Benue, Kanal Aminu Isa Kontagora ya fadawa wakilin sashen Hausa Hassan Maina Kaina a wata hira da suka yi cewa, ‘yan boko haram da suka saje da jama’a yanzu sun sake salon yakin sunkurun da su ke yi tun da an kwace garuruwan da a baya suka mamaye.

Kanal Aminu ya kuma ce idan mutane ba su tashi tsaye ba wajen bayyanawa jami’an tsaro wani abu da basu gane ba, irin wadannan hare-haren ba za su kare ba duk ko da cewa hukumomin tsaro na da bangaren dake kula da binciken sirri.

Game da hare-haren da aka kai a unguwar Jiddari Polo da jami’ar Maiduguri kwanan nan, inda mayakan suka toshe ramukan da aka gina kewayen birnin Maiduguri, Kanal Aminu ya ce akwai sakaci a wannan lamarin. Korar ‘yan boko haram daga dajin Sambisa ba yana nufin anyi maganin yakin sunkuru bane. Ya kuma ce idan ba zaman sulhu ‘yan boko haram suka nema ba, ko gafarar ‘yan Najeriya, har yanzu da sauran runa a kaba.

Kanal Aminu ya ce yanzu dole ne sojoji su canza salon yaki, ya kuma kara jaddada rawar da jama’a za su taka wajen bada bayani, saboda mayakan za su cigaba da nunu cewa har yanzu suna da karfi ta kai harin sari ka noke.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG