Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Australia Na Tuhumar Wani Jigo a Fadar Vatican Kan Laifin Lalata


Cardinal George Pell
Cardinal George Pell

A karon farko, an samu wani babba daga cikin makusantar Paparoma Francis a cikin zargin yin lalata a Fadar Vatican. Daya daga cikin abubuwan da Paparoman ya sha alwashin maganacewa a lokacin da ya karbi ragamar jagorancin Vatican shi ne kakkabe wadanda ake zargi da irin wannan laifi.

‘Yan sandan kasar Australia na tuhumar wani babban jigon fadar Paparoma dake Vatican da laifin yin lalata.

Hukumomi dai ba su ba da wani karin bayani akan zarge-zargen da ake yi wa Cardinal George Pell ba, baya ga cewa an sami korafe-korafe da yawa kan masu alaka da zargin.

A yanzu dai an umurci Cardinal Pell, wanda ya taba zama babban mai ba Paparoma Francis shawara akan harkokin kudi, ya bayyana gaban wata kotu a birnin Melbourne ranar 18 ga watan Yuli.

A wani taron manema labarai da aka yi a fadar Vatican, Pell ya fadi cewa bai aikata laifukan da ake tuhumarsa da su ba, kuma an dade ana kokarin a zubar mai da mutunci.

Cardinal Pell dai shi ne kusar Katolika a fadar Paparoma mafi babban mukami da aka taba zargi da irin wannan laifi mai alaka da jima’i a tarihin fadar.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG