Hezbollah Ta Ce Ta Kaddamar Da Wani Hari Ta Jirgin Sama Mara Matuki A Arewacin Isra'ila

Isra'ila

Kungiyar Hezbollah ta kasar Labanon ta ce ta kaddamar da wani harin jirgin sama mara matuki a safiyar yau Litinin a arewacin Isra'ila, inda sojojin Isra'ila suka ce harin ya raunata dakarunta biyu tare da ta da gobara.

Rikicin dai ya zo ne a daidai lokacin da ake fargabar barkewar yaki a yankin bayan kashe wani babban kwamandan kungiyar Hezbollah a kasar Lebanon a makon da ya gabata da kuma jagoran siyasar Hamas a Iran.

Sojojin Isra'ila a Iyaka da 'yan kungiyar Hezbollah

Kungiyar Hezbollah da ke samun goyon bayan Iran a cikin wata sanarwa ta ce ta kai hari kan wani sansanin soji da ke arewacin Isra'ila ne a matsayin martani ga hare-hare da kashe-kashen da Isra'ila ta kai a wasu kauyuka da ke kudancin Lebanon.

Da alama dai harin bai kasance wani mataki na ramuwar gayya da ake sa ran za ta dauka ba dangane da kisan kwamandan Hezbollah Fouad Shukur a birnin Beirut a makon jiya.

Isra'ila da Hezbollah dai sun shafe watanni 10 suna musayar wuta sakamakon yakin da ake gwabzawa a Gaza, amma a baya sun ajiye rikicin a wani mataki mai sauki wanda bai rikide zuwa yaki ba.

Kisan gillar da aka yi wa jagoran siyasar Hamas Ismail Haniyeh a Tehran babban birnin Iran a makon da ya gabata da kwamandan Hezbollah Shukur a Beirut ne ya tayar da tarzoma a yankin. Isra'ila dai ta na zama shirin mayar da martani daga Iran da mayakan sa kai na kawayenta.

-AP