WASHINGTON, D. C. - Wannan dai shi ne na baya-bayan nan a jerin munanan hadurran kwale-kwale da ke kara bayyana kasawar tsarin kula da bin doka a kasar.
Ana jigilar fasinjojin ne daga gundumar Borgu ta jihar Neja zuwa wata kasuwa da ke makwabciyar jihar Kebbi a yammacin ranar Litinin, lokacin da jirgin ya kife a kogin Naija, kamar yadda kakakin hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Neja Ibrahim Audu ya bayyana.
"An yi wa kwale-kwalen lodi fiye da kima don haka ne iska mai karfi ta shafe su suka kife," in ji Audu.
Ya ce karfin kwale-kwalen shi ne daukar fasinjoji 100, amma an kiyasta cewa yana dauke da adadi mai yawa, baya ga buhunan hatsi, lamarin da ya sa da wuya a iya daidaita shi lokacin da ya fara nutsewa.
Mazauna kauyukan na taimakawa 'yan ninkaya da jami’an agajin gaggawa don nemo fasinjojin da suka bata, wadanda yawancinsu mata ne, in ji Audu. To sai dai bai bayyana adadin mutanen da suka tsira ba.
Hadurran kwale-kwale ya zama ruwan dare a cikin al'ummomi yankunan karkara a fadin Najeriya, inda mazauna yankin da ke bukace da hanyar kai kayayyakin amfanin gonakinsu zuwa kasuwa, su kan yi cunkoso a cikin kwale-kwalen kirar gida sakamakon rashin kyawawan titunan mota.
Kawo yanzu dai babu tabbataccen adadin wadanda suka mutu a wadannan hadurran, ko da yake an sami akalla hatsari biyar da suka hada da fasinjoji akalla 100 kowanne a cikin watanni bakwai da suka gabata.
-AP