Shugaban rundunonin sojin Kenya Janar Francis Ogolla ya rasu a wani hatsarin jirgi mai saukar ungulu.
Shugaban Kenya William Ruto ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis.
Hatsarin ya faru ne da yammacin Alhamis kuma Shugaba Ruto ya ayyana zaman makokin kwanaki uku a duk fadin kasar.
Janar Ogolla mai shekaru 61, na rangadin yankin yammacin kasar ta Kenya wanda ke fama da matsalar ‘yan bindiga a lokacin da hatsarin ya faru.
Jirgin mai saukar ungulu na dauke ne da mutum 11 ciki har da Janar Ogolla a lokacin da ya fado kasa ya kama da wuta a kusa da kan iyakar kasar da Uganda.
Mutane tara ne suka mutu a hatsarin in ji Shugaba Ruto.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a san abin da ya haddasa hatsarin ba.
Ogolla ya rasu ya bar matarsa Aileen da yara biyu da jika daya.