Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kenya Ta Fara Mika Gawarwakin 'Yan Kungiyar Asiri 429 Ga 'Yan Uwansu


Kenya Attack
Kenya Attack

A ranar Talata ne gwamnatin Kenya ta fara mika gawarwakin 'yan kungiyar asiri 429 ga 'yan kungiyar asiri da ake musu shari'ar da ta girgiza kasar.

Gawarwakin da aka tono daga wani yankin karkara mai fadin gaske a gabar tekun Kenya sun nuna alamun yunwa da shakewa. Ana zargin shugaban kungiyar asiri Paul Mackenzie cewa shine yasa mabiyansa da su kashe kansu da yunwa domin saduwa da Yesu kuma yanzu haka yana fuskantar tuhume-tuhume da suka hada da kisan kai.

Paul Mackenzie shugaban wata kungiyar asiri a Kenya
Paul Mackenzie shugaban wata kungiyar asiri a Kenya

Hukumomi suna amfani da gwajin kwayoyin halitta ta DNA don taimakawa gano gawarwaki da iyalansu. A ranar Talata ne aka mika gawarwakin farko ga ‘yan uwansu. Hankali ya tashi sosai a dakin ajiyar gawarwaki na Malindi yayin da iyalai ke tattara 'yan uwansu don su sake binne su.

Francis Wanje, wani mahaifin ne da ya rasa ‘yarsa da wasu ‘yan uwansa bakwai.

Wanje ya ce: "Mun rasa mutane takwas daga cikin ‘yan uwanmu." "Ya kamata mu samu gawarwaki biyar, amma an fada mana cewa daya daga cikin yaran bai dace da DNA din mu ba.

An tuhumi Mackenzie da abokan aikinsa da dama a watan Fabrairu da laifin azabtarwa da kisan yara 191. Za a fara shari'ar a ranar 23 ga Afrilu. Ministan cikin gida Kithure Kindiki ya ayyana cocin Mackenzie na Good News International Ministries, a matsayin kungiyar miyagu.

Wasu 'yan Kenya da suka fusata sun yi mamakin yadda hukumomi ba su lura da wata alamar mace-macen jama'a ba tun da farko.

Hukumar kare hakkin dan Adam ta Kenya a makon da ya gabata ta ce ‘yan sanda sun gaza daukar mataki kan rahotannin da aka kai sanu da ka iya hana mace-mace a yankin Shakahola mai nisa. An bayar da rahotanni da dama a ofisoshin 'yan sanda daga mutanen da 'yan uwansu suka shiga cikin dajin.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG