Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Ghana Da Kenya Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Hadin Gwiwa


Williams Ruto da Nana Akufo Addo
Williams Ruto da Nana Akufo Addo

Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo da na Kenya, William Ruto, sun shaida hakan inda Ministar harkokin wajen Ghana, Shirley Ayorkor Botchwey, da sakataren majalisar ministocin harkokin wajen Kenya, Dokta Musalia Mudavadi, suka jagoranci rattaba hannun

Kasar Ghana da Kenya sun kara habaka huldar diplomasiya da tattalin arziki, ta hanyar rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da za ta tabbatar da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu da burin nemo hanyoyin da kasashen za su bunkasa huldar kasuwanci, tattalin arziki da zamantakewa a tsakaninsu. Kasashen biyu sun rattaba hannu kan wasu yarjeniyoyi 7 da suka hada da ilimi, yawon bude ido, tsaro, da inganta zuba jari, masana'antu, kere-kere da kasuwanci, a yayin ziyarar kwanaki uku da shugaban kasar Kenya, William Ruto, ya kai zuwa Ghana.

Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo da na Kenya, William Ruto, sun shaida hakan inda Ministar harkokin wajen Ghana, Shirley Ayorkor Botchwey, da sakataren majalisar ministocin harkokin wajen Kenya, Dokta Musalia Mudavadi, suka jagoranci rattaba hannu kan yarjejeniyar diflomasiya a fadar shugaban kasa, Jubilee House, dake birnin Accra.

Haka kuma an rattaba hannu kan wasu yarjeniyoyi da suka hada da ilimi, yawon bude ido, hadin gwiwa kan tsaro, kasuwanci da zuba jari, masana'antu da gudanar da mulki domin karfafa alakar dake tsakanin kasashen biyu.

A wani taron manema labarai na hadin gwiwa, shugaba Akufo-Addo ya ce, ‘Huldar kasuwanci da tattalin arziki tana ci gaba da bunkasa a tsakanin kasashen Ghana da Kenya, inda kasashen biyu ke kara fahimtar juna da kuma nuna goyon baya ga juna a kungiyoyin kasa da kasa da suka hada da MDD, Tarayyar Afirka, da kungiyar kasashen renon Ingila, na Commonwealth’.

A nasa bangaren Shugaba Ruto ya bayyana cewa, ‘yancin zirga-zirgar jama’a tsakanin Ghana da Kenya ya haifar da fa’ida sosai a fannin kasuwanci, zuba jari, da kuma yawon bude ido.

“A dangane da haka, ni da mai girma shugaban kasa, mun lura cewa, kasuwanci tsakanin Kenya da Ghana ya bunkasa a shekarar 2022, misali, a shekarar 2022, Kayayyakin da Kenya ta shigo da su cikin Ghana sun kai na dalar Amurka miliyan 10.4, kuma an kiyasta wasu kayayyakin da ake shigo da su a kan dalar Amurka miliyan 4.8.”

Wani mai sharhi kan harkokin siyasar cikin gida da ketare, Malam Issah Abdul Salam yace,sakamakon alaka da aka dora tsakanin Ghana da Kenya, ya sa shugaba William Ruto ya zo Ghana don kara jaddada alaka mai kyau dake tsakanin su tun da jimawa. Kuma wannan ziyarar za ta aka kara bunkasa sha’anin, ‘ilimi, yawon bude ido da ba da dama ga ziyarar kasashen juna, abubuwa ne da za su samar da mafani masu dimbin yawa tsakanin Ghana da Kenya”.

Masani kan harkokin kudi da kasuwanci, Hamza Attijjany, yace kasashen biyu za su amfana ta bangaren tattalin arziki, musamman a kasuwanci da bas hi da shinge tsakanin kasashen Africa, da kasar Ghana da Kenya suka runguma da hannu biyu-biyu. Yace, ‘A lokacin da kasar Kenya ta fara yin batir, Ghana ce kasa ta farko da aka fara yiwa talla don kasuwanci. Lallai Ghana da Kenya za su samu ci gaban tattalin arziki da ma nahiyar Afirka baki daya’.

Al’ummar kasashen biyu, za su samu alfanu idan an tabbatar da wadannan yarjejeniyoyin, in ji mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Malam Issah Mairago Gibril Abbas,wanda yace daliban kasashen biyu za su samu damar zurfafa iliminsu ta hanyar yarjejeniyar; haka kuma ‘yan kasuwar kasashen za su ci moriyar shirin nan na cinikayya tsakanin kasashen Afrika mara shinge AfCFTA.

A yayin ziyarar shugaba Ruto, ta kwanaki ukun, ya ba da lecca a hedkwatar AfCFTA ya kuma ziyarci kabarin tsohon shugaban Ghana, Kwame Nkrumah, a birnin Accra. Daga bisani Ghana ta karrama shi da babbar karramawa mai daraja, wato Companion of the Order of the Star of the Volta.

Domin karin bayani saurari rahotan Idris Abdullah.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:49 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG