Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalibai 11 Sun Mutu, 42 Sun Jikkata A Wani Hatsarin Motar Bas A Kenya


Kenya
Kenya

Wata motar bas da ke dauke da dalibai daga babbar jami'ar Kenya ta yi karo da wata babbar mota a kan wani babban titi, inda 11 daga cikinsu suka mutu, yayin da 42 suka samu munanan raunuka.

WASHINGTON, D. C. - Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya ce hatsarin ya afku ne da misalin karfe 5:50 na yamma (1450 GMT) a ranar Litinin a Maungu mai tazarar kilomita 360 daga Nairobi babban birnin kasar. Motar dai na dauke ne da daliban jami'ar Kenyatta da ke kan hanyar zuwa garin Mombasa da ke gabar teku.

Rundunar ‘yan sandan ta ce mutane 10 ne suka mutu nan take sakamakon karon sannan dayansu ya mutu daga baya a asibiti, inda ya kara da cewa mutane 42 ne suka samu munanan raunuka.

Mahukuntan kasar sun ce ana ruwan sama ne mai karfi, lokacin da direban motar bas din ya kokarin wuce wasu jerin motoci. Sai dai motar bas din ta kubce inda ta zarce zuwa gefen dama na titin, hakan ya sa direban motar ya nemi kauce wa yin karo da ka amma haka ya sa ya bugi bangaren hagu na bas din

Motar bas din tana dauke ne da mutane 58 a lokacin balaguro na ilimi.

Kungiyar agaji ta Red Cross ta Kenya ta shaida akan shafint na X cewa an kai wadanda suka jikkata asibiti a garin Voi da ke kusa da inda lamarin ya afku

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG