A yayin da ake gudanar ta babban taron majalisar dinkin duniya ba jihar New York ta kasar Amurka, shugaban kasar Iran Hassan Rouhanni ya bayyana wa sauran shugabannin duniya da suka halarci taron matsayar kasar sa dangane da shirn makamin Mukiliyas.
Shugaban ya bayyana cewar “ina mai tabbatar maku da cewa kasar Iran baza ta kasance, kasar farko wadda ta keda ka'idar yarjejeniya ba, amma zata maida matarnin daya kamata akan duk wani bangaren da yayi.
Abin takaici ne idan wannan yarjejeniyar ta wargaje ta dalilin baki a siyasar duniya.
Kalaman Rouhani, martani ne ga shugaba Trump na Amurka, wanda ya bayyanawa shugabannin jiya laraba cewar yarjejeniyar dage takunkumin tattalin arziki da aka kakabawa Iran domin ta dena shirin ta na nukiliya, ita ce yarjejeniya mara kangado da Amurka ta taba kulawa.