Ma’aikatan agaji sun cigaba da aiki yau Laraba a birnin Mexico da jihohin dake kusa da babban birnin kasar, suna fatan gano mutanen dake raye bayan girgizar kasa mai karfin maki 7.1 da ta faru a yanken, wadda ta yi sanadiyar mutuwar mutane 217 ta kuma lalata gine-gine dayawa.
Ministan harkokin cikin gidan kasar Mexico Miguel Osorio Chong ya ce sojan kasar da jami’an ‘yan sanda zasu cigaba da aikin neman mutane har sai sun bincike kowanne lungu da sakon da ake kyautata zaton za a gano karin mutanen dake da rai.
Fararen hula suma sun hada hannu da ma’aikatan agaji jim kadan bayan faruwar girgizar jiya Talata da rana, inda suka yi amfani da manyan na’urori da kuma hannayensu wajen kawas da baruguzan gine-gine.
Ya zuwa safiyar yau Laraba, shugaban cibiyar tsaron dakarun na musamman Luis Felipe Puente, ya fada a shafinsa na twitter cewa, an sami rahoton mace-mace 86 a birnin Mexico, 71 a jihar Morelos, 43 a jihar Puebla, 12 a jihar Mexico, 4 a jihar Guerrero sai kuma mutum daya a jihar Oaxaca.
Hukumomin kasar Mexico sun ce girgizar kasar da ta faru tayi sanadiyar mutuwar mutane dayawa.
WASHINGTON DC —
Facebook Forum