A bayan fagen taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya, an yi wani taro tsakanin mambobin Kungiyar Tarayyar Afirka da jami’an Majalisar Dinkin Duniya don tattauna yadda kasashen Nahiyar Afirka za su dada amfana da Majalisar Dinkin Duniya da kuma yadda su kuma kasashen na Nahiyar Afirka za su kara azama wajen bayar da gudunmowarsu ga cigaban Majalisar da ma duniyar baki daya.
Shugaban kungiayr Tarayyar Afirka (AU) kuma Shugaban kasar Guinea Alfa Konde, ya ce akwai bukatar sake tsari a kungiyar ta AU. Yan a mai nuni da irin fafatukar da ake yi kan ta’addanci a nahiyar da kuma bukatar da ke akwai ta a kara azama wajen aiwatar da abubuwan kawo cigaba a Afirka.
Kodayake tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo bai yi jawabi a wurin taron ba, ya bayyana ma wakilinmu a hirar da su ka yi da shi cewa dimokaradiyya ta dan bambanta daga kasa zuwa kasa;
Abokin aikinmu Sarfilu Hashim Gumel, wanda ya wakilci Sashin Hausa na wannan gidan rediyon, shi ne ya hada ma na wannan rahoton, kuma ga shi da cikakken bayanin:
Facebook Forum