Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kalubalanci matakin gwamnatin India na korar yan kabilan Rohingya a kotu


Yan Kabilar Rohingya a India
Yan Kabilar Rohingya a India

An shigar da wata kara a kotun kolin India dake kalubalantar matakin gwamnatin kasar na korar yan kabilan Rohingya da suka kai dubu dari hudu da suka arce daga Myammar.

Kotun kolin ta kasar India ta fara sauraren wannan karar a yau Litinin.


A wata sanarwa da gwamnatin ta aikewa kotun tana cewar yan Rohingya baki ne da basu da izini kuma wasu acikinsu na iya zama babban barazana ga tsaron kasar India.


Lauyan dake wakiltan yan Rohingya yace dokokin India sun bada daman daidaita yancin da kuma walwala ga kowane mutum, har ma da wadanda bay an kasar ba.


Kotun zata ci gaba da sauraren wannan karar a wata mai zuwa.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG