Jagorar kasar Myanmar, Aung San Suu Kyi, ta ce gwamnatinta ta na Allah wadai da take hakkokin bil'adama da aka yi a yammacin jihar Rakhine, inda aka tilastawa Musulmi ‘yan kabilar Rohingya kusan 400,000 suka fice zuwa Bangladesh da ke makwabtaka da kasar.
A wani jawabi da ta yi a yau Talata a Naypyitaw, babban Birnin kasar a gaban wasu jami’an diplomisiyyar kasashen waje, jagorar, wacce ta taba lashe lambar yabo ta zaman lafiya, ta ce kasar a shirye take ta ba da dama kasashen waje su je su yi bincike.
Ta kuma ba da tabbacin cewa za su binciki duk wani zargin take hakkin bil adama da aka yi a kasar.
Sai dai ta ce, za su dauki mataki ne akan zarge-zargen idan har aka samu kwararan hujjoji, tana mai cewa za su samar da wani tsari wanda zai bai wa mutanen da suka tsere su dawo gida bayan an tantance su.
Aung San Suu Kyi ta kuma ce duk da rikicin da aka samu, akwai Musulmi ‘yan kabilar ta Rohingya da dama da suke zaune a jihar ta Rakhine kuma babu abinda ya same su.
Facebook Forum