Hare haren bama bamai guda biyu da aka kai a arewa maso yammaci da kuma kudu maso yammacin kasar Pakistan a jiya Laraba sun kashe akalla mutane arba’in da biyu, kuma fiye da mutane sittin sunji rauni.
A harin farko, wani mai harin kunar bakin wake ne ya kai hari birnin Pashewar ya kashe akalla mutane talatin da bakwai da raunana mutum arba’in da biyar. Wani babban jami’in yan sanda ya fadawa Muryar Amirka cewa harin ya auna wasu daruruwan mutane ne wadanda ke halartar jani’izar matar wani dan yakin sa kai wanda baya goyon bayan kungiyar Taliban.
Kungiyar Taliban tayi ikirarin cewa ita keda alhakin kai harin tana mai fadin cewa tana hukunta wadanda ke goyon bayan gwanati ne.
Kafofin asibiti sunce wasu daga cikin wadanda suka ji rauni suna cikin mawuyacin hari.
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Banki Moon yayi Allah wadai da harin.
A lardin Baluchistan dake kudu maso yammacin kasar kuma, akalla farar hula biyar ne suka mutu, goma sha takwas kuma suka ji rauni a lokacinda motarsa ta taka wata nakiya da aka bizne a yankin Dera Bugti.