Hukumomi a China sun ce wata girgizar kasa ta ruguza daruruwan muhallai da gine-gine ta kuma kashe a kalla mutane 24 a lardin Yunnan da ke kudu maso yammacin kasar, wanda kuma ke kusa da kan iyaka da kasar Burma.
Kafafen yada labaran gwamnati sun ce sama da mutane 200 ne kuma su ka sami raunuka. A halin da ake ciki kuma kasar ta China ta bayar da rahotun fuskantar gibi na kudi dala biliyan 7.3 a watan Fabrairu a harkar kasuwancinta, wanda shi ne gibin da kasar ta fuskanta tun bayan watan Maris na bara kuma shi ne gibi mafi girma a tsawon shekaru 7.
To saidai kwararru sun ta’allaka gibin kan tsaikon da aka samu a masana’antu a lokacin bikin sabuwar shekarar kasar kuma sun a sa ran komai zai daidaita nan da zuwa wata mai zuwa.
Kasar ta China ta yi shelar saman rarar dala biliyan 6.5 a watan Janairu. Masana harkokin tattalin arziki sun yi hasashen za ta sami rarar dala biliyan 4.9 a watan Fabrairu.
China ta sha fama da matsin lamban daga manyan abokan cinakayyarta cewa ta bar darajar kudadents ta hau ta kuma rage yin babakere a harkar cinakayya, wanda ya kai jimlar kudi dala biliyan 183 a bara.
Yawan karuwar kayakin da China ke sayowa ya shafi yawan rarar da ta ke samu a shekara-shekara, wanda ya kai dala biliyan 196 a 2009; dala biliyan 295 a 2008.