Kasar Japan ta ayyana dokar ta baci a ma’aikatun nukiliyarta biyu da aka sami katsewar wutar lantarki sakamakon gagarumar girgizar kasar da aka yi, da ta haifar da igiyar ruwa ta tsunami a tsibirin Honshu, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane dubu daya. Hukumomi sun ce ma’aikatun biyu da kamfanin wutar lantarki na kasar Tokyo ke gudanarwa a birnin Fukushima, sun lalace ne bayanda girgizar kasar mai karfin maki 8.9 ta ingizo ruwa a gabashin Honshu jiya da rana. Na’urorin sanyaya ma’aikatun suka daina aiki abinda yasa cibiyoyin suka dauki zafin gaske. Hukumomi sun ce sun saki tururi kadan daga ma’aikatun domin rage kazamin zafin da suke dauka. Jami’ai a kasar japan sun ce zafin da cibiyoyin suka yi ya ninka abinda ya kamata sau dubu daya. Abinda ya tilasta kimanin mutane dubu arba’in da biyar dake zaune a tazarar kilomita goma da ma’aikatun kaura. An gina ma’aikatun nukiliyan kasar Japan yadda zasu iya kashe kansu idan aka yi girgizar kasar, sai dai suna bukatar wutar lantarki domin sanyaya na’urorin.