Kiristoci ‘yan tsiraru da ‘yan rajin kare hakkin bil Adama a Pakistan sun fito kan tituna domin zanga-zangar nuna rashin jin dadin kashe ministan gwamnati kwaya daya kirista da aka yi a bayan da ya kalubalanci dokar sabo ta kasar.
Masu zanga-zanga a birnin Islamabad, inda aka kashe ministan ranar laraba, sun soki gwamnati a saboda ta kasa kare ministan ‘yan tsiraru Shahbaz Bhatti, wanda aka harbe a kusa da gidansa.
‘Yan majalisar dokoki daga bangaren ‘yan tsiraru na Pakistan sun fice lokacin wani zaman majalisa. Sun bukaci gwamnati da ta dauki duk matakin da zata iya domin hukumta wadanda suka yi kisan.
Firayim minista Yousuf raza Gilani, ya bayyana zaman makokin kwana uku domin jimamin dan siyasar da aka kashe, ya kuam lashi takobin murkushe ta’addanci da tsageranci a Pakistan. Tsagera masu alaka da taliban da al-Qa’ida sun dauki alhaki, su na masu fadin cewa sun kashe Bhatti ne a saboda ya nuna adawa da dokar sabo.