Hare-Haren Rundunar Sojin Saman Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda A Kaduna

  • VOA Hausa
JIRGIN YAKIN SOJIN SAMAN NAJERIYA

JIRGIN YAKIN SOJIN SAMAN NAJERIYA

Bangaren sojin sama na aikin wanzar da zaman lafiya na “Operation Whirl Punch” ya lalata cibiyoyin adana kayan aiki na ‘yan ta’adda a dajin Yadi dake karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

Sanarwar da mukaddashin jami’an hulda da jama’a na rundunar sojin saman Najeriyar, Group Kyaftin Kabiru Ali, yace samamen da aka gudanar a Juma’ar da ta gabata, 27 ga watan Satumbar da muke ciki, ya biyo bayan samun sahihan bayanan sirri dake nuna cewa akwai dimbin ‘yan ta’adda da makamai a dajin na Yadi.

Ya bayyana cewa rahotannin da aka samu daga majiyoyi masu zaman kansu, ciki har da al’ummar yankin dake ba da bayanai, sun tabbatar da cewa an lalata ma’ajiyar makamai ta ‘yan ta’addar tare da hallaka da yawa daga cikinsu.

“Tsananta tattara bayanan sirri da sanya idanu sun tabbatar da cewa akwai dimbin ‘yan ta’adda da baburansu a cikin dajin, “kamar yadda aka ruwaito wani bangare na sanarwar na cewa.

Sanarwar ta ci gaba da cewarkarin bayanan sirrin sun bayyana cewar ma’adanar makaman mallakin kasurgumin dan bindigar ce, Kadage Gurgu, na hannun daman Dogo Gide.

Har ila yau, bayanan sirrin da rundunar sojin saman ta samu sun nuna cewar, Kadage Gurgu, ya rika samarda mafaka ga manyan ‘yan ta’adda sakamakon munanan hare-haren da sojoji ke kaiwa a jihohin Sokoto da Zamfara.