A wani mataki na kakkabe ‘yan bindigar da suka addabi jama’a musamman a yankin arewacin kasar, gwamnatin Najeriya ta tura ministan tsaron kasar Bello Matawalle jihar Sokoto tare da manyan Hafsoshin tsaron Najeriya don yaki da ta’addanci.
Kwararru da masana harakokin tsaro a Nijar na ganin akwai bukatar gwmanatin Nijar a nata bangare ta dauki mataki a kan iyakokinta da Najeriya saboda yadda fatattakar ‘yan bindigar ka iya sanya su ketarawa zuwa wasu kasashen makwabtan Najeriya irin su Nijar, kamar yadda Emoud Issouf kwararre kan harakokin tsaro a Nijar ya bayyana.
Masanan na ganin akwai rawar da al’umma za su iya takawa a irin wannan yanayin da ake ciki na matakin Najeriya na yakar ‘yan ta’adda ta hanyar kwarmata labari ga jami’an tsaro akan duk wani mutunen da ba su yarda da shi ba in ji mohamed Dilla masanin harakokin tsaro a Agadas.
Kwararru da masana na ganin gyara alaka tsakanin kasashen Najeriya da Nijar ta fannin tsaro domin yin hadin gwiwar yaki da ta’addanci da kasashen biyu makwabtan juna ke fusakanta shi ne zai iya kawo karshen matsalar tsaro a kasashen.
Saurari cikakken rahoton Hamid Mahmoud:
Dandalin Mu Tattauna