Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Sanda Sun Cafke Matar Wani Babban Dan Bindiga Da Makamai A Zamfara


'Yan Sanda A Jihar Zamfara
'Yan Sanda A Jihar Zamfara

Jami’an tsaro na ci gaba da samun galaba a yaki da ‘yan bindigar da suke addabar jihar Zamfara, inda suke  dada kama su, da tarwatsa yunkurin su na Kai hare hare, da hana satar mutane da sauran munanan hare-hare.

Jami’an tsaro na ci gaba da samun galaba a yaki da ‘yan bindigar da suke addabar jihar Zamfara, inda suke dada kama su, da tarwatsa yunkurin su na Kai hare hare, da hana satar mutane da sauran munanan hare-hare.

Duk da cewa suna cigaba da kai hare haren a wusu wuraren da kuma tare hanyoyin mota, sai dai kuma sannu a hankali, dubun su ya fara cika sannan an fara samun sakamako mai kyau fadin a jihar.

Bayan nasarar kashe babban dan fashin dajin nan da suka yi a makon da ya gabata, jami'an 'yan sanda a garin Anka a karamar hukumar Anka ta Jihar ta Zamfarar, sun samu nasarar cafke mata da ‘ya’yan wani gawurtacen shugaban ‘yan ta'addan mai suna Kachalla Jijji, dauke da Harsashin bindiga a yayin da take tare da Sauran abokan tafiyar ta na safarar makamai.

Jijji ya shahara wurin kai hare haren shi a yankunan Anka, Bagega, da kewaye, har zuwa jihohin Neja da Kebbi.

Wadanda aka Kaman sun hada da Mamuda Makakari, matarsa Kuluwa Mamuda, da wata mata, dubun su ya cika ne a lokacin da suke kan hanyar zuwa sansanin ‘yan fashin dajin a kauyen Makakari.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, CP Shehu Muhammad Dalijan, ya tabbatar da kamen, sannan ya bayyana yadda aka yi wadanda ake zargin.

Ya ce, “wanda ake zargi Mamuda Sani Makakari ya tabbatar man dacewa ya Kai shekara uku (3) da fara aiki tare da ‘yan ta'adda, mun same shi da albarusai guda 441 wanda matar wani babban barawo Kachalla Jijji ta bashi. Shi Kachalla Jijji dan bindiga ne wanda ke aiki karkashin Babban Barawon da ya akayi nasarar kashe shi a makon jiya Kachalla Halilu Sububu.” Inji Kwamishinan Yan sandan CP Shehu Dalijan.

Har ila yau CP Dalijan ya yi karin haske akan mutanen da ake zargin sun yi yunkurin safarar alburusan zuwa Anka, wanda yace Matar Kachalla Jijji ce taje ta karbo alabrusan daga wani babban barowa a yankin Kaura Namoda da nufin kai su wata Dabar dake can Makakari ta Karamar hukumar Mulkin Anka.

Tun da farko, a cikin wani faifan bidiyo da ya yadu a shafukan sada zumunta, daya daga cikin wadanda ake zargin, Mamuda Makakari, ya ba da sanarwa yayin gudanar da bincike na farko, Mamuda Sani Makakari ya ce ya karbo sakon albarusan daga garin Gusau, don ya kai su Makakari, Sai dai yace bai san wanda ya bashi sakon ba kuma bai san wanda zai amshi sakon ba, amma ya ce yana da lambonin wayoyin su.

A halin da ake ciki dai al’ummar jihar Zamfara na cigaba da furta albakcin bakin su dangane da nasarorin da jami’an tsaro suka samu a baya-bayan nan. Inda wasu ke jinjina da goyon baya akan nasarorin da jamia’an tsaron ke samu tare yi masu addu'ar cigabada samun nasara.

A nasu bangaren, Fatihu Rabi'u Zawiyya Gusau da Bilyaminu Muhammad sun ce jami’an tsaro a Jihar Zamfara suna kokari sosai wanda kuma ya dace a basu Kwarin Guiwa don kakkabe Yan ta'addan da kuma dawo da zaman lafiya a jihar tare da jinjinawa mahukunta akan nasarorin da ake samu.

Sai dai yayin da mutane da yawa ke yaba wa kokari jami'an tsaron, wasu kuma sunyi kira ne da a kara samun hadin gwiwa tsakanin gwamnatocin jihohi da na tarayya domin kawar da ‘yan fashin dajin baki daya. Sun kuma jaddada cewa dole ne a dage a ci gaba dafatatakar 'yan bindigar har sai an samu cikakken zaman lafiya.

Sai dai a nata bangaren, wata dattijuwa mai suna Asma’u Kuryar Madaro cewa tayi, kamata yayi Shugaban Kasa Tinubu da gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal su kara dagewa don a dawo da cikakken zaman lafiya, sai kuma wani magidanci Abdullahi yace "na ji dadi amma akwai bukatar gwamnatin tarayya da na jihar ta Zamfara su zauna su fahimci juna domin a cigaba da yakar wadannan miyagun mutane.”

Jihar Zamfara dai na ci gaba da fama da matsalar rashin tsaro, sakamakon hare haren 'yan bindigar dake garkuwa da mutane da kisa da kuma haddasa tashe-tashen hankula, lamarin ya fara tsakanin makiyaya da manoma.

Inda hakan yasa wasu Kungiyoyin da ke dauke da makamai suka ci gaba da amfani da raunin dake tsakanin jami'an tsaron kasar, suka cigaba da cin karen su ba babbaka wajen kai hare hare da kisan mutanen da basu ji ba basu gani ba da lalata masu dukiyoyi da yin garkuwa da su don neman kudin fansa.

Ko da yake a 'yan kwanakin nan jami’an tsaro sun kara kaimi, don ganin anyi tunkare hanci.

A saurari rahoton Abdulrazak Bello Kaura:

‘Yan Sanda Sun Cafke Matar Wani Babban Dan Bindiga Da Makamai A Zamfara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:27 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG