Hare-haren da Isira’ila ta kai ta sama sun kashe akalla mutane 18 a Gaza, ciki har da hudu da ke neman mafaka a wani sansanin Falasdinawa da su ke gudun hijira a cikin wani ginin asibiti.
Har ila yau, wani harin wuka da wani Bafalasdine ya kai ya kashe mutane biyu a wata unguwa da ke wajen birnin Tel Aviv.
Tashin hankali ya kara ta’azzara bayan yakin kusan watannin 10 a Gaza da kuma kashe wasu manyan mayaka guda biyu a wasu hare-hare daban daban a kasashen Lebanon da Iran a makon da ya wuce.
Wadannan kashe-kashen sun kawo barazanar daukar fansa daga Iran da kawayenta da kuma sanya fagabar barkewar yakin da zai yi barna a yankin.
Wata mata ‘yar shekara 70 da wani mutum mai shekaru 80 ne su ka mutu a harin na wuka, a cewar hukumar agaji gaggawa ta Isira’ila Magen David Adom da wani asibiti da ke kusa, sannan wasu mutane biyu sun samu raunuka.
'Yan sanda sun ce wani Bafalasdine ne ya kai harin, wanda tuni aka kashe shi.
Masu aikin ceto sun ce an gano wadanda su ka jikkata ne a wurare daban-daban guda uku, kowane da nisan mita 500.
Da farko dai ‘yan sanda sun ce suna neman wasu wadanda ake zargi amma daga baya sun yi watsi da yiwuwar samun karin wani maharin.