Yankin Arewacin Najeriya dai har yanzu tsugune take duk da kokarin da hukumomi ke yi na shawo kan matsalar rashin tsaro, abin dai na ci gaba da gagara.
Yankin masarautar Zuru a jihar Kebbi na ci gaba da fuskantar barazana, domin ko a wannan mako mahara da aka kiyasta sun kai 300 bisa babura sun afka wa garin Unashi cikin karamar hukumar Danko Wasagu suka kashe mutane suka kora dabbobi.
Wani mazaunin yankin mai suna Babuga Unashi ya ce yanzu haka zaman zullumi ne kawai jama'ar yankin ke yi.
Shugaban kungiyar ‘yan sakai, Mani John ya ce da samun labarin kawo harin, ya sheda wa jami'an soji da ‘yan sandan kwantar da tarzoma da aka kai yankin, kuma yaran sa sun kai dauki.
Ya kara da cewa akwai matsalar da suka gano wadda watakila ita ce ke sa ana yawan kai hare hare a yankin.
Rundunar 'yan sanda ta jihar Kebbi, ta bakin kakakin ta DSP Nafi'u Abubakar, ta ce yawaitar irin wadannan hare hare da ake kaiwa yankunan jihar ya sa ta kirkiro da wani shiri da ta kira Operation Ganuwa.
Wadannan hare haren dai suna zuwa ne lokacin da aka girke jami'an ‘yan sandan kwantar da tarzoma a yankunan da ke fama da matsalolin rashin tsaron.
A saurari rahoto cikin sauti daga Muhammad Nasir:
Your browser doesn’t support HTML5
Karin bayani akan: Operation Ganuwa, Jihar Kebbi, Nigeria, da Najeriya.