Rundunar sojin ta karbi motoci kirar Hilux guda takwas da babura ashirin daga gwamnatin jihar Kebbi domin taimakawa wajen samar da tsaron jihar baki daya.
Tabarbarewar tsaro a Masarautar Zuru da ke kudancin jihar Kebbi ya yi sanadin mutuwar mutane da dama daga bangaren Dakarkari da Fulani Makiyaya wanda a da suke zaune lafiya har da auratayya tsakaninsu na tsawon fiye da shekara 100.
Wasu rahotanni daga bangarorin guda biyu, sun yi zargin cewa, an kashe al'uman Fulani da Dakarkari da yawan su ya wuce 174 a kananan hukumomin Sakaba, Danko-Wasagu, Fakai da Zuru wanda su ne kananan hukumomi hudu da ke karkashin Masarautar Zuru.
Ko a wani hari da aka kai baya bayan nan a garin Munhaye cikin yankin Danko Wasagu an kashe mutane hadi da soja biyu kuma aka kona motar Hilux ta Soji.
yan-bindiga-na-ci-gaba-da-kisan-mutane-a-arewacin-najeriya
yan-najeriya-sun-fara-daukar-matakin-kare-kan-su
an-kama-mutum-bakwai-a-sokoto-dake-da-hannu-a-garkuwa-da-dan-kasar-amurka-a-nijar
Bisa ga wannan matsalar da ma makamantan ta ne yasa gwamnatin jihar Kebbi ta tallafawa sojin da ke aiki a jihar.
Da ya ke hannun ta motoci hilux 8 da babura 20 ga kumandan burged ta daya Burgediya Genar Muhammad Bello Wabili, sakataren gwamnatin jihar ne Babale Umar Yauri yace gwamnati ta san da cewa wadannan ababen hawan sun yi kadan amma dai tana kokarin kara samar da wasu domin ta hakan ne zasu iya yin aikin su cikin nasara.
Sabon kumandan burget ta daya Burgediya janar Muhammad Bello Wabili wanda bai Jima da samun sauyin wurin aiki daga jihar Yobe ba, yace bayanin da ya samu da kama aiki a wannan burget ya nuna cewa, akwai bambanci ga tsaro idan aka kwatanta da inda ya fito amma dai yace dukan su akwai kalubale ciki.
Yace zai yi amfani da kwarewar aiki da ya samu daga yankin arewa maso gabashin Najeriya domin bada gudunmuwa ga magance matsalolin tsaro a yankin da dawo da aiki.
Jihar Kebbi na daya daga cikin jihohin da suka yi fama da hare haren ‘yan bidnga da ya janyo asarar rayuka da kaddarori, kamarin da ya jefa al’umma cikin zaman fargaba da zullumi da ya kuma durkusar da harkokin rayuwar yau da kullum a jihar.
Saurari rahoton Muhammadu Nasir cikin sauti.