Hankalinmu A Kan "Champions League" Yake Ba A Kan Mbappe Ba - Ancelotti

Carlo Ancelotti da 'yan wasan Real Madrid bayan da suka doke Bayern Munich a wasan semifinals na gasar zakarun turai

Ana dai ta hasashen Mbappe zai nufi gasar La Liga ne inda zai bugawa Real Madrid a kakar wasa mai zuwa.

Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya ce yayin da hankalinsu yake kan lashe wani kofin gasar Zakarun Nahiyar Turai ba shi da lokacin da zai kai hankalin nasa kan zuwan Kylian Mbappe a kakar wasa mai zuwa.

A ranar Juma’a Mbappe da ke taka leda a kungiyar Paris Saint-Germain ya sanar da cewa zai bar kungiyar ta Faransa.

Ana dai ta hasashen zai nufi gasar La Liga ne inda zai bugawa Real Madrid a kakar wasa mai zuwa.

Ancelotti ya bayyan hakan ne yayin wani taron manema labarai na farko da ya yi a ranar Asabar tun bayan da Mbappe ya sanar da shirin ficewarsa daga PSG, inda aka tambaye shi ra’ayinsa kan hakan.

Kocin na Madrid ya ce abin da yake so shi da tawagar ‘yan wasan su mayar da hankali akai shi ne ranar 1 ga watan Yuni, wato ranar da za a buga wasan karshe na gasar ta Zakarun Nahiryar Turai a London.

Real Madrid za ta kara ne da kungiyar Borussia Dortmund ta kasar Jamus a wasan na karshe.