WASHINGTON, D.C. - Shugaba Mohamed Bazoum, wanda aka zaba a dimokaradiyyance a wannan kasa ta Afirka ta Yamma, ana tsare da shi a fadar shugaban kasa da ke Yamai tare da matarsa da dansa tun lokacin da wasu bijirarrun sojoji su ka habarar da shi a ranar 26 ga Yuli.
Iyalan (na Bazoum) na rayuwa ne babu wutar lantarki kuma sai shinkafa da abincin gwangwani da ya rage kawai suke samun ci, in ji mai ba da shawara. Bazoum na cikin koshin lafiya a halin yanzu kuma ba zai yarda ya taba yin murabus ba, a cewar mai ba da shawara din, wanda ya yi magana bisa sharadin sakaya sunansa saboda bai da hurumin tattauna wannan batu mai sarkakkiya da manema labarai.
Jam’iyyar siyasa ta su Bazoum ta fitar da wata sanarwa da ta tabbatar da yanayin rayuwar shugaban kasar, ta kuma ce iyalan ma ba su da ruwan famfo.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya tattauna da Bazoum a ranar Talata game da kokarin diflomasiyya na baya-bayan nan, in ji mai magana da yawunsa, kuma Blinken "ya jaddada cewa lafiya da tsaron Shugaba Bazoum da danginsa su ne mafi muhimmanci."
A wannan makon, sabuwar gwamnatin mulkin sojan ta Nijar ta dauki matakin dora kanta a karagar mulki, ta kuma yi watsi da kokarin da kasashen duniya ke yi na shiga tsakani.
A ranar Litinin ne kuma Gwamnatin mulkin sojan kasar ta nada sabon Firai Minista, masanin tattalin arziki na farar hula Ali Mahaman Lamine Zeine. Zeine dai tsohon Ministan tattalin arziki ne kuma Ministan kudi wanda ya bar mulki bayan juyin mulkin da aka yi a baya a shekarar 2010 wadda ta hambarar da Gwamnati a lokacin. Daga baya kuma ya yi aiki a bankin raya Afirka.
-AP