Hamas ta sako wasu dattawan mata ‘yan Isra’ila su biyu a ranar Litinin yayin da Isra’ila ke ci gaba da luguden wuta a yankin Gaza.
Hakan na faruwa ne yayin da a gefe guda Amurka take nuna damuwa kan yiwuwar yaduwar rikicin na Isra’ila da Hamas a yankin Gabas ta Tsakiya.
Cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta ce ta saki matan ne a mataki na jin-kai.
Kungiyar ba da agaji ta Red Cross ta ce ta fitar da matan biyu, daya mai shekaru 85 daya kuma mai shekaru 79 daga yankin na Gaza a ranar Litinin.
A ranar Juma’a mayakan na Hamas suka fara sakin ‘yan Isra’ila biyu – wata mata da diyarta, kusan makonni biyu bayan da suka kai wani harin ba-zata da ya kashe Isra’ilawa sama da 1,400 mafi akasari fararen hula.
Sun kuma kama wasu mutum sama da 200.
Jami’ai a Washington sun ce sun aba Isra’ila shawara da ta jinkirta shirinta na kutsa kai cikin yankin na Gaza, domin a samu karin lokacin da za a tattaunawar sulhu don a sako sauran Yahudawan.
Duk wannan matsaya da Amurka ta nuna, dakarun Isra’ila sun kai hare-haren sama sama da 300 a ranar Litinin a yankin na Zirin Gaza.
Tura dakaru cikin yankin na Gaza kai ya dagula yunkurin da ake yi na tattaunawa don a sako mutanen, wadanda ake kyautata tsammanin wasunsu na cikin hanyoyi karkashin kasa da mayakan Hamas suka tona cikin shekaru da dama yayin da Isra’ila ta toshe hanyar ficewa ta Meditareniya.
Shugaban dakarun tsaron Isra’ila Yoav Gallant a makon da ya gabata ya sha alwashin cewa sama da dubu 300 da kasar ta girke a gefen yankin na Gaza za su kutsa cikin yankin, ba tare da ya ambaci lokacin da su dauki wannan mataki ba.
Su dai jami’an Amurka na fargabar yiwuwar yaduwar rikicin a yankin Gabas ta Tsakiya.