Idan har tayi nasarar, yarjejeniyar za ta kawo karshen yakin da ya ragargaje zirin Gaza da galibinsa birni ne, tare da hallaka fiye da mutane 46, 000, da kuma raba al’ummar yankin da yawansu kafin yakin ya kai mutum miliyan 2.3 da muhallansu sau da dama, a cewar hukumomin yankin.
Haka kuma za ta iya rage yawan zaman dar-dar da ake yi a gabas ta tsakiya, inda yakin Gaza ya kunshi Iran da kawayenta irinsu; kungiyar Hizbullahi ta Lebanon da Houthi ta Yemen da kungiyoyi masu fafutuka da makamai a kasar Iraki.
A cikin makonni 6 na gabar farko ta yarjejeniyar mai gabobi 3, Hamas za ta saki ‘yan Isra’ila 33 da take garkuwa dasu, da suka hada da dukkanin mata (sojoji da farar hula) da yara da kuma mazan da shekarunsu suka zarta 50.
Isra’ila za ta saki dukkanin matan Falasdinawa da yara ‘yan kasa da shekaru 19 da take tsare dasu a kurkukunta a karshen gabar farko ta yarjejeniyar. Adadin Falasdinawan da za’a saki zai ta’allaka ne kan yawan mutanen da ake garkuwa dasu da aka saki, kuma zai iya kasancewa tsakanin falasdinawa 990 zuwa 1, 650, ciki har da maza, mata da yara.
A sanarwar da ta fitar a yau Juma’a, Hamas tace an shawo kan matsalar da ta kunno kai dangane da wasu bangarorin yarjejeniyar tsagaita wutar ta gaza.
A zirin Gaza kuwa, jirgin saman yakin Isra’ila sun zafafa kai hare-hare, a yau Juma’a, hukumar bada agajin gaggawa ta farar hula tace an hallaka akalla mutane 101, ciki har da mata 58 da yara, tun bayan da aka sanarda batun kulla yarjejeniyar a Larabar da ta gabata.
-Reuters