Hakurin Amurka Ya Kusa Karewa Kan Korea ta Arewa - Nikki Haley

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Nikki Haley

Amurka ta ce shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un, ya kusa kure hakurinta duk da cewa ba wai Amurkan na son tsunduma cikin yaki ba ne, kamar yadda Jakadiyar kasar a Majalisar Dinkin Duniya, Nikki Haley ta fada.

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Nikky Haley ta ce Shugaban kasar Korea ta Arewa Kim Jong Un na neman fada ne da kudinsa, kuma ya kwan da sanin cewa Amurka ba ta da wadataccen hankurin ci gaba da jure wa hakan.

Jakadiyar ta ce yadda yake amfani da makamansa masu linzami ba bisa ka’ida ba ke nuna cewa yana rokon fada ne shi da kansa.

Ta ce yaki ba abu ne da Amurka ke fatar anin ta tsunduma cikin sa ba, sai dai ta kara da cewa amma kuma hakurin Amurka yana da iyaka.

Haley ta ce za su kare kansu dama kawayen su.

Jakadiyar ta Amurka dai tana magana ne a wajen wani taron gaggawa na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da aka kira jiya Litinin bayan da kasar Korea ta Arewa ta kammala gwada makamin ta na nukiliya na 6 a ranar Lahadi.

Kasar ta Korea Ta Arewa ta ce ta samu nasarar gwada wani gagarumin bam na “hydrogen” da za’a iya dasa shi akan makami mai linzame mai tafiya daga wata nahiya zuwa wata.

Koda yake masana basu tabbatar da hakan ba, amma dai sun ce wannan makamin na 6 shine ya fi duk wani wanda ta gwada a baya girma.