Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Korea Ta Arewa Ta Yi Gwajin Makami Na Shida


Shugaban Korea ta arewa Kim Jong Un zagaye da mukarrabansa a cibiyar kera makamin nukiliyan kasar, ranar 3, ga watan Satumbar 2017. KCNA via REUTERS
Shugaban Korea ta arewa Kim Jong Un zagaye da mukarrabansa a cibiyar kera makamin nukiliyan kasar, ranar 3, ga watan Satumbar 2017. KCNA via REUTERS

Wasu kasashen duniya da masana na fargabar cewa Korea ta arewa ta sake wani gwajin makami mai linzami sa'oi kadan bayan da ta sanar da cewa ta kera babban makamin kare dangi na hydrogen bomb.

Akwai alamu da ke nuna cewa Korea ta Arewa ta yi gwajin makamin nukiliya a karo na shida da tsakar ranar yau Lahadi agogon yankin, a cewar gwamnatocin Korea ta kudu da Japan da kuma sauran kwararru da ke nan Amurka.

A cewar kwararru a fannin lura da motsin kasa na Amurka da China, an ji rugugin kasa mai karfin maki 6.3 a yankin Punggye-ri da Korea ta arewa ke gwaje-gwajen makamanta.

Mintina biyar bayan hakan ne kuma, kwararrun suka ce sun ji karar girgizar kasa da karfinta ya kai maki 5, wanda ake kyautata zaton cewa karar rugujewar ramin da aka dasa makamin nukiliayan ne, bayan da aka harba shi.

Jeffery Lewis, kwararre a cibiyar nazarin yaki da yaduwar makaman nukiliya ta James Martin, ya ce sam bai zai yi mamaki ba, idan aka ce Korea ta arewan ta mallaki fasahar kera babban makamin kare dangi.

Wannan gwaji na baya-bayan nan, na zuwa ne sa’oi kadan bayan da kasar ta Korea ta arewa ta ce ta yi nasarar kera babban makamin kare dangi na hydrogen bomb, wanda za a iya dasa shi a jikin makami mai linzami da kan iya tafiya daga wata nahiya zuwa wata.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG