Gwmanatin tarayyar Najeriya ta ce ta cimma yarjejeniya da Hadaddaiyar Daular Larabawa na dage haramcin shiga kasar ga matafiya ‘yan najeriya daga yau 15 ga watan Yulin da muke ciki.
Ministan Yadda Labarai da wayar da kan al’umma, Mohammed idris ne ya bayana hakan a yau litinin da yake hira da manema labaran fadar shugaban kasa jim kadan bayan taron majalisar zartawa ta tarayya.
Hakan na zuwa ne watanni biyu da Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya bayyana shirin gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa, na dage haramcin bada biza ga ‘yan Najeriya, nan bada jimawa ba.
Keyamo, yayin wata ganawa da babban hadimin Shugaban Kasa Bola Tinubu, Otega Ogra, wacce aka wallafa a shafin fadar shugaban kasar na YouTube, yace an riga an cimma yarjejeniya tsakanin Shugaban Najeriya Bola Tinubu da takwaransa na Hadaddiyar Daular Larabawa Muhammad Bin Zayed Al-Nahyan a ziyarar da Tinubun ya kai kasar a watan Satumbar bara.
Ku Duba Wannan Ma Nan Bada Jimawa Ba Hadaddiyar Daular Larabawa Zata Dage Haramcin Baiwa 'Yan Najeriya Biza - Keyamo
Ku Duba Wannan Ma Emirates Zai Koma Jigila Tsakanin Legas Da Dubai A Ranar 1 Ga Watan Oktoba
A watan Mayu da ya gabata kamfanin jiragen saman Emirates ya bayyana cewar zai cigaba da ayyukansa a Najeriya tun daga ranar 1 ga watan Oktoba mai zuwa, inda zai fara zirga-zirga tsakanin biranen Legas da Dubai a kullum.
A sanarwar daya fitar a yau Alhamis, kamfanin jiragen saman, dake da tushe a Hadaddiyar Daular Larabawa, ya bayyana cewar zai cigaba da jigila ne da jirgi samfurin boeing 777-300er.
Idan ba a manta ba shekaru biyu da suka gabata ne Hadaddiyar Daular Larabawan ta yanke shawaran haramta wa ‘yan Najeriya takardan izinin shiga kasar.