Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Matakan Da Ya Kamata A Dauka Kafin A Koma Baiwa ‘Yan Najeriya Biza Zuwa Dubai - Ministan Harkokin Waje


Ministan Harkokin wajen Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar
Ministan Harkokin wajen Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar

Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar ya ce akwai matakan da ya kamata a dauka kafin gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa ta koma baiwa ‘yan Najeriya takardar izinin shiga kasar.

Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar ya ce akwai matakan da ya kamata a dauka kafin gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa ta koma baiwa ‘yan Najeriya takardar izinin shiga kasar.

“An samo bakin zaren. Akwai ‘yan matakan da ya kamata a dauka. Akwai sa hannu da za a yi a wasu takardu da wasu makamantan su. Akwai ziyara da yakamata su kawo mana, (kuma) mai yuwa mu ma mu kai musu. An kasha maganan kenan sai dai a koma ba da biza”, a cewarsa yayin wata hira ta musamman da wakilin Muryar Amurka, Victor Mathias a birnin Washington, DC.

Hakan na zuwa ne kwanaki bayan da kamfanin jiragen sama na Emirates ya ce zai cigaba da ayyukansa a Najeriya daga ranar 1 ga watan Oktoba mai zuwa, inda zai fara zirga-zirga tsakanin Legas da Dubai a kullum.

Ministan ya kara da cewar “ba yanda za a yi jirgin sama ya fara zirga-zirga tsakanin Najeriya da Hadaddiyar Daular Larabawa ba tare da an koma ba da biza ba.

“Amma wannan abu ne da ya juma muna tattaunawa tsakanin mu kasashen biyu. Bana son ni ince ga abun da zai faru, sai idan mu da su mun yadda akan matakan da za a dauka, ga ainihin rana da za a koma yin kaza da kaza da kaza suma sai su koma su fada”

Ministan yace da farko abun da ya kara bata tsakani shine yadda wasu ‘yan Najeriya mazauna kasar suka shiga harkokin da ya saba wa al’adu da doka da oda a Hadaddiyar Daular Larabawar irin su safarar miyagun kwayoyi, da sata da makamantansu.

Ya kuma tabattar cewar “in an koma bada biza, ya kasance wanda suke samun bizan nan, ‘yan Najeriya ne masu bin doka, masu bin ka’ida. Wadanda idan suka tafi kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ba zasu shiga wani mummunan sana’a ba ko kuma dabi’unsu su kasance suna karya dokokin wancan kasar ba wadda ko a Najeriya ba za mu yadda a karya wadanan dokokin ba”.

A kwanakin baya mabambantan ra’ayoyi daga 'yan Najeriya sun biyo bayan sanarwar kamfanin jiragen saman Emirates na Shirin dawo da jigilar fasinjoji tsakanin kasashen biyu inda wasu suka koka akan yadda kamfanin ta ki bayyana shawarar da ta yanke akan baiwa matafiyan Najeriya biza ba, sa’ilin da wasu suka yi murnar dawowar zirga-zirgar.

Akwai Matakan Da Ya Kamata A Dauka Kafin A Koma Baiwa ‘Yan Najeriya Biza Zuwa Dubai - Ministan Harkokin Waje
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:49 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG