Ma'aikatar Kula da Ma'adinan Kasar Nijar ta bada umarnin rufe kamfanin kasar China mai suna Sahara SARL, bayan samun sa da laifin gurbata muhalli da kuma zubar da guba wacce tayi sanadiyyar mutuwar dabbobi da dama.
Hakan ya biyo bayan ziyarar gani da ido, bisa rakiyar jami'an 'yan sanda da ke binciken lamarin, jim kadan bayan ta tabbatar da zargin da makiyayan sukayi na cewa guba na halaka musu dabbobi
Kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun jima suna kokawa da yadda kanfanonin kasashen waje dake hakar ma’adinai ke gurbata muhalli.
Sulaimane Boube mai fafutukar kare hakkin bil’adama a Agadas ya bayyana gamsuwar sa da wannan matakin
Kungiyoyin dai sun jaddada bukatar tallafin gwamnati ga wadanda abin ya shafa domin taimaka musu maye gurbin dabbobin su da suka mutu
A saurari cikakken rahoton Hamid Mahmoud:
Your browser doesn’t support HTML5