Ta hanyar wata wasika da suka aike wa jakadan China a ranar Litinin 6 ga watan Mayu ne hukumomin jamhuriyar Benin suka sanar da daukar matakin hana jigilar danyen man Nijar da ya kamata a fara fitarwa zuwa kasuwannin duniya. Wannan wata hanya ce da shugaba Patrice Talon ya bullo da ita da nufin matsa lamba ga hukumomin mulkin sojan Nijer don ganin sun bude iyakar kasar da ke ci gaba da kasancewa a rufe.
Wata majiya a ma’aikatar man fetur ta ce ya zuwa wannan lokaci Nijar ba ta samu takardar da ke sanar da cewa Benin ta dauki wannan mataki ba, to amma wani jigo a kungiyar Front Patriotique ta masu goyon bayan CNSP Bana Ibrahim, na ganin matakin na Benin magana ce ta tsakaninta da China.
Barazanar kutsen da aka yi hasashen za a iya fuskanta daga dakarun da Faransa ta girke a Benin ne hukumomi suka ayyana a matsayin dalilinsu na karfafa matakan da suka dakatar da zurga zurga ta bangaren Nijar yayin da a bangaren Benin ake kallon abin tamkar wani matakin huce takaici sakamakon yadda shugaba Talon ya kasance na gaba gaba lokacin da CEDEAO ta kakaba wa Nijar takunkumi. Masanin tattalin arziki kuma mai sharhi kan al’amuran kasa da kasa Issoufou Boubacar Kado, na ganin ya kamata kasashen 2 su jingine dukkan wasu bambance bambance don neman mafita.
Tashar jirgin Ruwan Cotonou ita ce mafi kusa ga ‘yan kasuwar Nijar kuma ta na samun galibin kudaden shigarta daga kayayyakin da ‘yan Nijar ke oda daga waje, a saboda haka rufe iyaka a tsakanin Nijar da Benin yau akalla watanni 9 mataki ne da ya matukar haddasa koma bayan tattalin arziki ga kasashen 2 makwaftan juna.
A shekarar 2019 ne Nijer da China suka cimma wata yarjejeniya da kasar Benin wacce a karkashinta aka amince wa kamfanin CNPC na hadin gwiwar Nijar da China da ya shimfida bututun mai, mai tsawon kilomita kusan 2,000 a wani yunkurin fitar da man kasar zuwa kasuwannin duniya, aikin da ya kammala a watan Disamban 2023 da nufin fara loda man a watan Mayu daga tashar jirgin ruwan Seme.
A watan Afrilun da ya shige gwamnatin Nijar ta sanar da cin bashin dala miliyan 400 daga kasar China da za a yi amfani da su wajen biyan danyen mai a tsawon watanni 12.
Saurari cikakken rahoton:
Dandalin Mu Tattauna