Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Na Fuskantar Koma Bayan Yancin 'Yan Jarida A Kasashen Sahel


An Gudanar Da Shagulgulan Bikin Ranar ‘Yancin ‘Yan Jarida A Nijar
An Gudanar Da Shagulgulan Bikin Ranar ‘Yancin ‘Yan Jarida A Nijar

A yayin da kasashen duniya ke bukukuwan karrama ranar ‘yancin aikin jarida a yau 3 ga watan Mayu, rahotanni na nuni da cewa ‘yancin aikin jarida da ‘yancin fadin albarkacin baki na fuskantar barazana a kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso.

Garkame ‘yan jarida akan aiki da matakan rufe kafaffen labaran kasa da kasa na neman zama ruwan dare a yankin Sahel.

Idan aka ci gaba da tafiya a haka ka iya tsunduma al’umomin kasashen Sahel cikin halin rashin samun ingantattun labarai a daidai lokacin da masu yada labaran bogi a kafaffen sada zumunta ke fadada ayyukansu.

Ranar yancin 'yan jarida da ke matsayin ta yin bitar yanayin da fannin ke ciki ta zo wa ‘yan jaridar yankin Sahel a karkace.

Yanzu haka ana tsare da wasu ‘yan jarida 2 a hannun mahukuntan Nijar da suka hada da Ousman Toudou wanda a baya ya rike mukamin mashawarci ga shugaba Issouhou Mahamadou da shugaba Mohamed Bazoum da mawallafin jaridar l’enqueteur Soumana Idrissa Maiga.

Ana zargin ‘yan jarida da rubuta labarin da aka kira mai barazana ga sha’anin tsaro.

Kungiyar ONIMED mai alhakin zuba ido akan ayyukan kafaffen labarai da shiga tsakani a ta bakin shugabanta, Jafar Maman, ta nuna damuwa da abinda ke faruwa a kasar da a wani lokaci ta sha yabo sakamakon sakar wa ‘yan jarida mara.

An Gudanar Da Shagulgulan Bikin Ranar ‘Yancin ‘Yan Jarida A Nijar
An Gudanar Da Shagulgulan Bikin Ranar ‘Yancin ‘Yan Jarida A Nijar

Wata matsalar da ta karu akan wadanda ‘yan jarida ke fuskanta a yau itace, wasu na amfani da kafaffen sada zumunta don cin zarafin ‘yan jarida da nufin huce takaici a bisa zargin bada labarin da ba su ji dadinsa ba.

Editan jaridar La Roue de l’Histoire Info, Ibrahim Moussa shi ne sakataren kungiyar ‘yan jarida mai kula da tsaro da zaman lafiya RJSP, ya ce duk yanda ka yi aikin ka na dan jarida akwai wadanda za su tsane ka har ma wasu suna tura maka sakwannin barazana.

A Burkina Faso kuwa gwamnatin rikon kwaryar kasar ta kaddamar da matakan rufe kafaffen kasa da kasa bayan da suka bada labarin da ya fito a rahoton kungiyar kare hakkin bil adama ta HRW kan zargin jami’an tsaro da kisan wasu farar hula, yayin da a Mali aka saka wa kafafen labarai takunkumin da ya hana masu bada labarin da ya shafi aiyukan ‘yan siyasa a bisa hujjar dakatar da aiyukan jam’iyu. Lamarin da a fili ke gwada girman koma bayan da ake fuskanta a yankin da ke matukar bukatar aiyukan fadakarwa game da matsalolin tsaro.

An Gudanar Da Shagulgulan Bikin Ranar ‘Yancin ‘Yan Jarida A Nijar
An Gudanar Da Shagulgulan Bikin Ranar ‘Yancin ‘Yan Jarida A Nijar

Malan Zabeirou Souley shine shugaban kungiyar ANEPI ta mawallafan jaridu ta kasa ya kuma ce barazanar da ake yi wa ‘yan jarida, dama ce ake bai wa masu shiga yanar gizo su yi ta wallafa labaran bogi .

Yancin aikin jarida da yancin fadin albarkacin baki ma’auni ne na mizanin dimokradiya a kasashen da ke karkashin mulkin farar hula abin da ke zama tamkar wata hanyar zuba ido kan aiyukan gwamnati ta yadda za a gudanar da lamuran mulki a karkashin doka da mutunta ‘yancin talaka.

Shimfida kyaukyawar mu’amula da ‘yan jarida abu ne da ya wajaba ga gwamnatocin mulkin soja a matsayinsu na wadanda suka sha alwashin mutunta yarjejeniyoyin kasa da kasa.

An Gudanar Da Shagulgulan Bikin Ranar ‘Yancin ‘Yan Jarida A Nijar
An Gudanar Da Shagulgulan Bikin Ranar ‘Yancin ‘Yan Jarida A Nijar

A sanarwar farko da suka fitar sojojin majalissar CNSP sun jaddada aniyar mutunta yarjeniyoyin kasa da kasa da Nijar ta yi na’am da su.

Gwamnatin rikon kwarya ta hanyar ministan sadarwa ta sha nanata aniyar bai wa ‘yan jarida damar yin aiki ba tare da wata tsangwama ba, sai dai rufe cibiyar ‘yan jarida ta Maison de la Presse a karshen shekarar da ta gabata, mataki ne da ake ganin ya haddasa koma bayan mu’amula a tsakanin mahukunta da shugabanin kungiyoyin ‘yan jarida a wani lokacin da kasar ta bullo da wata sabuwar tafiya dake hangan kwato ‘yancin kai na zahiri daga turawan mulkin mallaka.

Saurari rahoton Souley Moumouni Barma cikin sauti:

Yau Take Ranar 'Yancin 'Yan Jarida
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:21 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG