Kokarin gujewa rikici ya sa gwamnatin Niger, ta shirya taro da ilahirin shugabannin addinin Islama domin nazarin hanyoyin rigakafi, inji ministan cikin gida Bazoum Muhammaed.
Ministan ya ce yanzu kasar ba ta da wani tsari akan yadda za'a bude masallaci da kuma yadda za'a yi wa'azi, kowa ya ga dama sai ya bude masallaci kuma ya yi wa'azi yadda ya ke so a cewar Bazoum Muhammad. Haka ma mutane su kan tashi su je fili su kama yin wa'azi ba tare da tambayar kowace hukuma ba. Har ma gidajen rediyo da talibijin suke shiga su yi wa'azi ba tare da wani izini ba, inji ministan.
Irin masu yin wa'azi yadda suka ga dama su kan yi alfani da kalamun da basu dace ba su harzuka mutane.
Shugaban wata kungiyar Islama Shaikh Nuhu Abdulrahaman, ya yaba da yunkurin wanda ya kira "babbar shawara ce suka kawo ga kasarmu". Ya ce shawarar za ta tabbatar da kwanciyar hankali a cikin kasar.
Shi ma Uztaz Muhammad Ashiru Muhammad Tukur, na wata kungiya kuma reshen Maradi ya gargadi gwamnati ta dauki matakan da zasu ba da damar cin moriyar shirin. Ya yi kira ga gwamnati kada ta bari harkokin addinin su lalace. Kungiyarsa ta yi murna gwamnati za ta sa tsari akan gina masallatai da yin wa'azi.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5