Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya gana da takwaran aikinsa na Burkina Faso Roch Marc Christian Kabore a yau Talata cikin rangadin da zai kai shi kasashen Afirka uku.
Cikin abubuwan da aka gudanar a yau sun hada da jawabi ga daliban jami'a da kuma ganawa da 'yan Faransa da ke zama a Ouagadougou, babban birnin kasar.
Cikin muhimman batutuwa da aka fi maida hankali akai yayin wannan ziyara akwai batun tsaro, da samar da ayyukan yi, da muhalli, da kuma batun 'yan ci-rani.
Tattaunawa akan Matasan Afrika na daya daga cikin muhimman batutuwan da aka maida hankali akai har ila yau a lokacin taron koli na hadin gwiwa tsakanin jami'an Tarrayar Turai a Ivory Coast a gobe Laraba.
Daga bisani Shugaban na Faransa zai kai ziyara Ghana, ziyarar da babu shugaban Faransa da ya taba kaiwa.
A ziyarar shugaban na Faransa zai gana da matasa a Accra, babban birnin Ghana inda nan ne zai zamanto zangonsa na karshe.
Faransa na da dakurun sama da 7,000 a Afirkaa, hade da wadanda ke farautar ‘yan ta’adda a yankin Sahel, da hadin gwiwar sabuwar rundunar yaki da 'yan ta'adda da Macron ya taimaka wajen kafa ta.
Facebook Forum