Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rantsar Da Uhuru Kenyatta a Wa'adi Na Biyu


Mutane 60,000 ne suka cika makil a dandalin taro na kasa da ake kira Kasarani domin halartar bikin ranstar da shugaba Uhuru Kenyatta a wa'adi na biyu. Sai dai magoya bayan shugaban 'yan adawa Raila Odinga sun yi arangama da 'yan sanda.

An rantsar da shugaban Kenya Uhuru Kenyatta a yau Talata a wa'adi na biyu, bayan wani zazzafan zabe da aka yi da ya rarraba kawunan 'yan kasar.

Kotun kolin kasar ta yi watsi da sakamakon zaben farko da aka yi, da kuma kauracewa zaben da 'yan hamayya suka yi.

Rahotanni sun ce 'yan sanda sun yi amfani da borkono mai sa hawaye a wani bangaren babban birnin kasar na Nairobi domin tarwatsa magoya bayan madugun 'yan adawa Raila Odinga, wadanda suka yi gangami.

Sun gudanar da gangamin ne domin tunawa da wadanda suka rasa rayyukansu a arangama daban-daban da jami'an tsaro suka yi a lokacin zaben kasar a baya.

Kenyatta ya lashe zaben da aka yi cikin watan Agustan da ya gabata, amma kotun Kolin kasar ta yi watsi da sakamokon zaben saboda kurakurai da kotun ta ce an tafka a yayin tattara kuri'u a hukumar zaben kasar.

Odinga, bai tsaya takara ba a lokacin da aka sake gudanar da zaben, kuma ya umarciu magoya bayansa da su kauracewa zaben saboda a cewar shi zaben "shirme" ne kawai.

Masu sharhi sun ce babban kalubalen da Kenyatta zai fuskanta shi ne yadda zai hada kan kasar wacce suke ganin an samu rarrabuwar kawuna.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG