Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Fafutuka a Nijar Za Su Ci Gaba Da Kalubalantar Kasafin Kudin 2018


Shugabannin Niger
Shugabannin Niger

Majalisar dokokin kasar Nijar ta amince da kasafin kudin shekarar 2018 da bangaren gwamnati ya gabatar mata duk da korafe-korafen da jama'a su ke yi akan wasu matakan da gwamnati za ta dauka da ake ganin za su cutar da talakawa.

Tun kafin majalisar dokokin Nijar ta amince da kasafin kudin shekarar 2018, kungiyoyin kare hakkin dan Adam suka gargade ta da kada ta amince da shi saboda wasu dokokin da kasafin ya kunsa da suke ganin za su cutar da talakawan kasar.

To sai dai majalisar ba ta yi aiki da shawarwarin kungiyoyin farar hula da na 'yan rajin kare hakkin dan Adam ba.

"Bayan zamanta (majalisa) ta yi na'am da kasafin," inji Suraji Isa.

A cewar Suraji Isa duk da cewa bakin gwamnati da na 'yan majalisa ya zo daya akan kasafin wadanda suke mulki a kansu, kimanin mutane miliyan 20, basu yadda ba.

Ya ce saboda haka yanzu suka ja daga da gwamnati da 'yan majalisa. Ya ce a cikin kasafin kudin za'a zalunci talaka da kasar gaba dayanta.

Amma a nasa ra'ayin, Inusa Ona, wani dan farar hula yana cewa duk wani cece-ku-ce akan kasafin kudin shekarar 2018 ya kare, zartas da abin da kasafin ya kunsa shi ne gwamnati za ta sa gaba.

Ya ce kuma musanta abubuwan da aka ce an saka cikin kasafin kudin.

Sai dai kungiyoyin da suke adawa da kasafin sun sha alwashin fantsama kan hanyoyi su nuna rashin amincewarsu tare da nufin tankwaso gwamnati ta canza ra'ayi.

Ga rahoton Sule Barma da karin bayani:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00

Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG