WASHINGTON, D.C. - Gamayyar kungiyoyin ‘yan kasuwa da na ‘yan kwadago sun gudanar da zanga-zanga a fadin kasar sakamakon dakatar da tallafin man fetur.
Kungiyoyin sun kuma nemi da a kara musu kudi akan mafi karancin albashin ma'aikatan gwamnati.
A wannan makon, kungiyoyin suka yi kira da a gudanar da yajin aikin gargadi na kwanaki biyu.
Ministan kwadago da samar da ayyukan yi Samuel Lalong ya shaidawa Muryar Amurka cewa gwamnati ta gana da wakilan kungiyar kwadago a ranar Talata, kuma kungiyar ta amince ta ba gwamnatin kasar mako biyu domin ta magance wasu korafe-korafen na su.