Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Likitoci Zasu Fara Zanga-Zanga A Kullum A Ma’aikatun Lafiya Don Tilasta Biya Masu Bukata


Likitocin Najeriya yayin wata zanga-zanga da suka yi (Hoto: Channels TV)
Likitocin Najeriya yayin wata zanga-zanga da suka yi (Hoto: Channels TV)

Kungiyar likitocin Najeriya ta sanar da sabon matakin tsunduma zanga-zanga a kewayen ma’aikatun lafiya a fadin Najeriya don tilastawa hukumomi biyawa likitocin bukata.

Kungiyar likitocin Najeriya ta sanar da sabon matakin tsunduma zanga-zanga a gewayen ma’aikatun lafiya a fadin Najeriya don tilastawa hukumomi biyawa likitocin bukata.

Zanga-zangar da kungiyar likitocin ta kira da ta lumana zata fara ne daga ranar Laraba 9 ga watan Agusta 2023.

Wannan ya biyo bayan matakin da gwamnatin Najeriya ta yi niyar dauka na cewa baza ta biya albashi ga ma’aikatan da ba sa zuwa aiki ba wato wadanda suka auka yajin aiki kamar yadda kungiyar likitocin ta yi.

Mataimakin sakataren kungiyar likitoci masu neman kwarewa NARD Dr. Nura Umar ya ce tsaida biyan albashin ma’aikatan da gwanatin ta ce zata yi tamkar barazana ce, kuma hakan ba zai hana su gwagwarmaya da jajircewa wajen neman hakkin su ba.

Dr. Nura Umar, ya kara da cewa likitocin za su yi zanga-zangar ne don su nuna fushin su tare da yin Allah wadai da gwanatin da bata damu da al'ummar ta ba, inda ya ce idan aka cigaba a haka, za a wayi gari babu likitoci da za su duba marasa lafiya a asibitocin kasar.

Kamar dai yadda gwamnatin Najeriyar ta yi a gargadin aukawa zanga-zangar ‘yan kwadago na daukar matakan hana zanga-zangar ta hanyar cigaba da tattaunawa, har yanzu irin matsayar gwamnatin kenan kan matakan ma’aikatan.

Idan za’a iya tunawa likitocin sun sanar tsunduma yajin aiki na sai baba ya gani ne tun a ranar 26 ga watan jiya.

Saurari rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:37 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG