ABUJA, NIGERIA - A zantawarsa da Sashen Hausa na Muryar Amurka, Mataimakin Sakataren kungiyar ta likitoci masu neman sanin makamar aiki ta NARD Dr. Nura Umar, ya ce daga cikin dalilan da ya sa suka tsunduma cikin wannan yajin aiki sun hada da karancin likitoci, rashin biyan wasu hakkokinsu da suka hada da na jarabawa da kuma sauran alawus-alawus.
Ya kara da cewa akwai kuma matsalar ficewa kasashen ketare da abokanan aikinsu ke yi, lamarin da ya haddasa yawan aiki da likitoci ke yi.
Sakataren kungiyar ya ce idan ba’a manta ba, kungiyar ta yi yajin aikin gargadi na kwanaki biyar a watan Afrilu na wannan shekarar inda ta zauna da Gwamnatin Najeriya akan bukatun nasu da suka dade suna bibiya kuma aka cimma yarjejeniya amma abin ya ci-tura na rashin cika alkawari daga Gwamnati.
Dr. Nura Umar ya ce kungiyar tasu ta yi la’akkari da cewa masu karamin karfi su ne ka fama da rashin lafiya saboda karancin likitocin da rashin kayan aiki a asibitoci ya sa mutane suna rasa ransu, ga kuma cire tallafin man fetur da ya haifar da tsadar rayuwa.
Daga karshe Dr. Umar ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta duba mutanen kasa da su kansu Likitoci ta biya musu koda wasu daga cikin hakkokin nasu.
Idan za’a iya tunawa kungiyar Likitocin na NARD ta fara nuna bukatar a biya mata wadannan bukatun nata ne tun a shekarar 2014.
Saurari ciakken rahoto daga Hauwa Umar:
Dandalin Mu Tattauna