Gwamnatin Kamaru na iya kokarinta ta hanyar jaddada tsaro akan iyakokinta da Najeriya. Sojojin ta na filin fage dare da rana musamman ma a arewacin kasar inda suke cigaba da samun nasara kan ‘yan kungiyar Boko Haram da suke kokarin shigowa kasar ta Kamaru.
A kwanan baya wasu sojojin Najeriya sun nemi mafaka a kasar Kamaru. Haka ma ranar Talatar nan da ta wuce an sami labarin cewa wasu sojojin Najeriya su 321 sun shiga garin Mora dake Kamaru.
A halin da ake ciki dai yanzu, ba a wasa da duk wani labari da aka samu musamman akan baki ko wasu wadanda ba a gane masu ba don farauto 'yan kungiyar Boko Haram. Shi ya sa ma ake gudanar da bincike a kasar.
To sai dai wadansu kuma na amfani da wanna yakin da gwamnati ke yi don cutar wasu, wani abu da ya faru da Mallam Idi. Shi dai Mallam Idi ya shaida a wata hira da suka yi da wakilin muryar Amurka da ke Kamaru Mohammadu Danda cewa, an yi binciken shi ciki-da-bai bisa ga zargin da wasu da ya kira makaryata da makiya suka yi masa na ce wa shi dan kungiyar Boko Haram ne. Amma bisa ga dukan alamu, mallam idi ya fita daga wannan zargin tunda dai hukuma da jami’an tsaron kasar basu ce masa uffan ba. Kuma ya yi kira da jama’a da su daina yi masa kazafin cewa shi dan Boko Haram ne.
Ga Mohammadu Danda da Mallam Idi.
Your browser doesn’t support HTML5