Kakakin sojojin Najeriyan Manjo Janaral Chris Olu Kolade yayi magana akan labaran yadda sojoji ke arcewa daga faggen daga wai suna kokawa kan rashin ingancin makamai, aukawa tarkon makirai da rashin armashin alawus.

Yace kawai soja ya gudu daga inda aka turashi aiki ya je yana yada karerayi kan abun dake faruwa a faggen daga domin a ce shi jarumi ne yakamata akai rahoton irinsu a gaban hukuma domin a damkesu a hukumtasu. Chris Kolade yace wanda ya gudu ko bayan yayi shekara ashirin yana aiki matsayinsa daya ne domin ya aikata mummunan laifi ga kasa.

Bayyanan labarin arcewar sojojin Najeriya dari biyar da suka fada kasar Kamaru na kara nuna irin fargabar da a keyi da yadda 'yan kungiyar Boko Haram ke kara karfi.

Tuni dai rundunar sojoji tace ba haka labarin yake ba. Abun da ya faru sojojin sun yi ja da bayan rago ne kuma dabara ce da zasu juyo domin cin nasara.

To saidai irin wadannan korafe-korafe ba ga sojoji kawai suka tsaya ba har ma da 'yansanda. Biyo bayan harin da aka kai kan cibiyar horas da 'yansandan kwantar da tarzoma a Gwoza jihar Borno ya sanya wani da yake ikirarin saje ne na 'yansanda ya bugo waya. Ga abun da yake cewa "Domin za'a yi recrutment na 'yansanda ko na soja Najeriya ba zata sami wanda zai fito ya shiga aikin dan sanda koko aikin soja ba domin muna mutuwa. Ba makamai ake bamu ba. Yanzu wadanda suka bata wadanda ba'a san idan suke ba ...Na taba fita da wani kwamanda a Buni Yadi. Lokacin da abun bai yi zafi ba 'yan tada kayar baya suka fito suna harbi. Mun bisu...Mutanen nan suka bata a gidaje... Hanset nashi yayi ringing sai yaji wani mutum yana cewa kai ne unit kwamanda kaza, sai yace ee. Yace to ka withdrwaing mutanenka. Unit kwamanda yace ranka ya dade kai waye ne sai mutumin ya kashe wayarsa. Ya zo yana gwada lambar a gabanmu taki tafiya".

Sajen yana zaton wadan ya buga wayar yana cikin wadanda suke da hannu a cikin masu tayar da kayar baya. Yace a cikin jami'an tsaro akwai wadanda suke da hannu dumu-dumu a cikin abun dake faruwa.

'Yansandan kwantar da tarzoma sun samu kawar da 'yan kalakato ko maitatsine a Kano, Maiduguri, Gombe da Yola a farkon shekarun 1980. Amma bayan shekaru ashirin ga sojoji da 'yansanda tun 2009 suke ta fafatawa amma ba sauki a lamarin tamkar ciwon dankama.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.

Sojan da Ya Gudu Daga Bakin Daga Ya Aikata Mummunan Laifi ga Kasarsa - 3' 05"

Kakakin sojojin Najeriya Chris Olu Kolade yace idan soja mai nuna bijirewa ne ko ya arce daga faggen daga ko ya nuna fargaba kiman sojan ta zube warwas.
WASHINGTON, DC —